Lakurawa sun kashe ’yan canji 2 suna tsaka da cin kasuwa a Sakkwato

[ad_1]



Maharan da ake zargin ’yan bindigar Lakurawa ne sun kai hari shagon canjin kuɗi a kauyen Durusar Gawo da ke Ƙaramar Hukumar Gudu ta jihar Sakkwato, inda suka kashe mutum biyu sannan suka raunata ɗaya.

Rahotanni sun ce ’yan ta’addar sun kuma kwashe kuɗi masu yawa lokacin harin.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga yankin ne da misalin ƙarfe 2:50 na rana, kuma kai tsaye suka nufi ɓangaren masu canjin kuɗi a kasuwar garin.

A cewarsa, ’yan bindigar da suka kai harin kusan su 11 ne, suka fara harbe-harbe kan ’yan kasuwa da mazauna yankin, inda suka kashe manyan ’yan kasuwa biyu, Alhaji Ummaru da Alhaji Sani, waɗanda aka sani da sana’ar canjin kuɗi a yankin.

“Sun kashe Alhaji Ummaru da Alhaji Sani nan take. Daga bisani suka harbi wani mutum, sannan suka kwashe kuɗin Nijar masu yawa yayin da jama’a suka gudu suka bar shagunan su,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa daga baya wasu biyu daga cikin maharan suka dawo a kan babur, suka ce wa jama’a su koma kasuwa domin sun riga sun kammala abin da suka zo yi.

“Bayan sun tafi, mun rufe shagunanmu, kowa ya gudu don tsira. Har yanzu babu jami’an tsaro da suka iso yankin,” in ji shi.

Shaidar ya ce maharan sun kai irin wannan hari a kasuwa da kauyukan makwabtan yankin a ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka yi garkuwa da dabbobi masu yawa.

Mazauna yankin sun koka kan tabarbarewar tsaro, suna masu cewa suna buƙatar kariya fiye da ayyukan gine-gine.

“Muna buƙatar tsaro fiye da komai. A wajenmu, kamar babu gwamnati a kasa saboda ba mu san daɗin dimokuraɗiyya ba. An tilasta rufe makarantu saboda rashin tsaro, kuma jama’a na rayuwa cikin tsoro,” in ji wani mazaunin yankin.

Shi ma wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce babu jami’an tsaro a Kurdula, hedikwatar gundumar Durusar Gawo.

“Nisan Kurdula da Balle kusan kilomita 45 ne, kuma hanyar ta lalace. Kafin jami’an tsaro su iso, maharan sun riga sun gama aikinsu sun tsere,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gundumar Bacaka ce kaɗai ke da ɗan tsaro, amma mazauna yankin suna dogaro da taimakon Arewa Dandi a Jihar Kebbi saboda kusanci.

Mazauna yankin sun roƙi Gwamnatin Jihar Sakkwato da hukumomin tsaro da su gaggauta kai musu dauki.

Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, DSP Ahmad Rufa’i, bai yi nasara ba har zuwa lokacin da haɗa wannan rahoton.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *