An rufe wurin haƙar zinare a Kebbi

[ad_1]



Gwamna Nasir Idris ya ba da umarnin gaggauta rufe wurin haƙar zinare da ke Mararrabar Birnin Yauri a Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi.

Yayin da yake ba da wannan umarnin, ya ce an dauki matakin ne domin kawar da matsalar haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da kuma daƙile duk wata barazana da za kawo tarnaƙi a cikin al’umma.

Aminiya ta ruwaito cewa, ziyarar bazata da gwamnan ya kai cibiyar haƙar zinaren a ranar Alhamis, na zuwa ne bayan rikicin da aka yi tsakanin mazauna yankin da kuma jami’an gwamnatin tarayya da ke aiki a wurin.

A cewarsa, za a ci gaba da harkar haƙar zinare da zarar an samu maslaha tsakanin gwamnatin Kebbi da kuma jami’an da ke aiwatar da shirin gwamnatin tarayya na haƙar zinare wato PAGMI.

Gwamnan ya kuma bai wa ma’aikatar haƙar maadanai ta jihar umarnin tattara bayanan duk wasu mutane, ƙungiyoyi ko kamfanoni da ke da rajistar haƙar zinare ko wasu ma’adanai a kowane sassa na Jihar Kebbi domin tsaftace harkar.

Ya bayyana cewa “ba za mu zuba ido wasu mutane daga ƙasashen ƙetare irin su Mali, Tanzania, Chadi da Nijar su riƙa shigowa suna haifar da barazanar tsaro a jiharmu ba.”

Ana iya tuna cewa, da yammacin Lahadin da ta gabata ne aka saka dokar hana fita a garin Yauri da ke Jihar Kebbi bayan wani tashin hankali tsakanin masu haƙar zinare da matasan gari, abin da ya yi sanadin mutuwar wani matashi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *