Majalisar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi Naira biliyan 75

[ad_1]



Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 na Naira biliyan 75 na kasafin kuɗin jihar da ƙananan hukumomi.

An amince da kasafin kuɗin ya zama doka ne a yayin zaman majalisar wanda mataimakin Shugaban Majalisar Hon. Sani Isiya ya jagoranta.

Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar wanda Hon Ibrahim Hamza Adamu ya gabatar.

Ƙarin kasafin kuɗin da aka amince da shi ya ƙunshi Naira biliyan 58 na Gwamnatin Jiha da kuma Naira biliyan 17 na Ƙananan Hukumomi 27, wanda ya ƙunshi kashe kuɗaɗe na yau da kullum da na manyan ayyuka.

A cikin jawabinsa, Mataimakin Shugaban Majalisar ya bayyana cewa, bisa wata wasiƙa da aka samu daga ɓangaren zartarwa, an yi shirin ƙarin kasafin ne domin magance matsalolin kuɗi da suka kunno kai.

Yin hakan zai haɓaka ayyuka da shirye-shiryen da ke gudana a cikin fannoni masu mahimmanci kamar: ilimi da kiwon lafiya da ababen more rayuwa da noma.

Majalisar dai ta amince da ƙarin kasafin kuɗin na shekarar 2025, wanda ya kai Naira biliyan 689.3 kuma majalisar ta amince da shi tun a ranar 31 ga Disamba, 2024.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *