Gwamnatin Katsina ta kori ma’aikata da malaman makaranta na bogi 3,488

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga ƙananan hukumomi 34 da hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi (LEA) bayan wani binciken tantance su ya bankado badakala.

Gwamnan jihar, Dikko Radda, wanda ya karɓi rahoton kwamitin a ranar Laraba, ya ce an tantance ma’aikata 50,172, inda aka tabbatar da sahihancin 46,380, yayin da sauran suka bayyana da takardun bogi, takardun daukar aiki na ƙarya, wasu kuma suka ki bayyana a gaban kwamitin.

An gabatar da rahoton a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar, inda manyan jami’an gwamnati da mambobin kwamitin tantancewa suka halarta.

A cewar rahoton, a karon farko a tarihi, an samar da kundin bayanan dukkan ma’aikatan a intanet, kuma ana sa ran samun rarar Naira miliyan 453.3 a kowane wata idan aka aiwatar da shawarwarin kwamitin.

Kwamitin mai mambobi 10 ya gano takardun haihuwa na bogi, ɗaukar ma’aikata ƙasa da shekarun da doka ta tanada, yin karin matsayi ba bisa ka’ida ba, da kuma bayar da guraben aiki ga wasu maimakon ainihin wadanda aka ɗauka.

Haka kuma, an dawo da Naira miliyan 4.6 daga hannun jami’ai da ke karɓar albashi sau biyu ko kuma suna karɓar albashi yayin da suke hutun aiki.

Shugaban kwamitin, Abdullahi A. Gagare, ya bayyana cewa an bankado Sakataren Ilimi na Zango LEA da ake zargin ya haɗa baki da wasu don saka ma’aikata 24 na ƙarya, yana mai cewa hakan “babban cin amanar aiki ne.”

Gwamna Radda ya ce, “Mun daɗe a cikin tsarin, kuma mun san irin waɗannan abubuwa suna faruwa. Mutane da dama sun yi korafi, har ma sun gargaɗe ni cewa aikin kwamitin zai iya lalata siyasar da nake yi kuma ya janyo min faduwa zaɓe.

“Amma duk da haka ban damu ba, domin halin da Katsina ke ciki yana buƙatar gyara tsarin da yin abin da ya dace.”

Gwamnan ya kuma ce a halin yanzu ƙananan hukumomi sun sami rarar kudi har kusan Naira miliyan 500, wanda zai kai Naira biliyan 5.7 idan aka aiwatar da shawarwarin kwamitin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *