Uwar jam’iyyar NNPP ta soke dakatar da Dungurawa daga shugabancinta a Kano

[ad_1]



Kwamitin Zartarwar jam’iyyar NNPP ya yi watsi tare da soke korar da aka yi wa shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, inda ya ce matakin ba ya bisa ka’ida.

A cikin wata sanarwa da aka fitar daga sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja a ranar Litinin, NNPP ta ce matakin da wasu shugabannin jam’iyyar na gundumar Gargari, ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano suka ɗauka, ya saba wa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Sanarwar da mai magana da yawun NNPP na ƙasa, Bamofin Ladipo Johnson ya sanya wa hannu, ta ce kwamitin ya yi Allah-wadai da wannan mataki matuka inda ya jaddada cewa shugabannin gunduma ba su da ikon dakatarwa ko cire shugaban jiha.

“Kwamitin Zartarwar NNPP na Ƙasa na ya yi Allah-wadai da korar da aka yi ikirarin yi ga shugaban NNPP na jihar Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, yana mai cewa wannan mataki ba daidai ba ne, karya tsarin dimokuraɗiyya ne, kuma babu wani tasiri da zai haifar,” in ji sanarwar.

Me sauya sheƙar Abba zai haifar a siyasar Kano?

A cewar jam’iyyar, matakin da shugabannin gundumar Gargari suka ɗauka ya babban laifi ne, saboda ya saba tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Kwamitin ya kuma yaba da jagorancin Dungurawa, inda ta bayyana shi a matsayin shugaba mai kishi a aiki, mai jajircewa da bin doka, wanda jagorancinsa ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa da ci gaban jam’iyyar a jihar Kano.

Lamarin dai ya zo ne a a daidai lokacin da rikice-rikicen cikin gida duka dabaibaye NNPP a Kano, sakamakon sabani kan shugabancin jam’iyyar da kuma jita-jitar yiwuwar sauya shekar Gwamnan jihar da akasarin masu rike da mukamai a jam’iyyar, zuwa jam’iyyar APC.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *