Ba Mu Da Shirin Mayar da Nijeriya Ƙasa Mai Jam’iyya Ɗaya – APC
[ad_1]
Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa babu shirin mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya, duk da cewa wasu ‘yan siyasa da dama sun bar jam’iyyun adawa tare da koma wa APC.
Sakataren yaɗa labarai na APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce jam’iyyar ba ta da niyyar daƙile jam’iyyun adawa, kuma canjin jam’iyya abu ne na al’ada a tsarin dimokuraɗiyya.
- Jami’ar MDD: Kasar Sin Babbar Ginshiki Ce Ta Cinikayyar Duniya
- Kotu Ta Tisa Ƙeyar Malami Zuwa Gidan Yarin Kuje
Morka ya bayyana cewa APC ce jam’iyyar da aka zaɓa a zaɓen shugaban ƙasa na baya, kuma mutane na da ‘yancin canza jam’iyya bisa doka.
Ya jaddada cewa a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Nijeriya, mayar da ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba zai yiwu ba.
Ya ƙara da cewa dimokuraɗiyya na bai wa mutane damar yin zaɓinsu, kuma shiga APC da ‘yan siyasa ke yi wani ɓangare ne na tsarin dimokuraɗiyya, ba barazana ga jam’iyyun siyasa ba.
[ad_2]
Source link