Haraji: Gwamnati Ba Za Ta Cire Kuɗi Kai-Tsaye Daga Asusun Bankin Mutane Ba – Oyedele
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa sabbin dokokin haraji da za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026, ba za su haɗa da cire kuɗi kai-tsaye daga asusun banki na mutane ba.
Shugaban Kwamitin Haraji na Fadar Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce mutane za su bayyana kuɗin shigarsu da kansu sannan su biya haraji a inda ya dace.
- Sin Ta Gudanar Da Kananan Ayyukan Amfanar Da Jama’a A Dukkanin Sassan Duniya A Shekarar 2025
- An Yi Taron Ayyukan Noma Na Kwamitin Tsakiyar Kasar Sin A Beijing
Ya bayyana cewa tsarin yana da sauƙi, bayyananne, kuma ba zai wahalar da talakawa ba.
Oyedele ya ƙara da cewa masu ƙananan sana’o’i da waɗanda ke da ƙaramin albashi za su fi amfana, saboda dokokin sun tanadi kariya ga masu rauni kuma sun tabbatar da adalci a biyan harajin.
Shugaba Bola Tinubu ma ya tabbatar da cewa za a aiwatar da sabbin dokokin haraji kamar yadda aka tsara, duk da sun fuskanci suka daga wasu ƙungiyoyi.
Ya ce dokokin na nufin sauƙaƙa tsarin haraji, tallafa wa kasuwanci, da ƙarfafa tattalin arziƙi.
Gwamnati ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su goyi bayan dokokin, tana mai jaddada cewa za su rage nauyin haraji, kare masu ƙaramin albashi, da kuma bunƙasa tsarin haraji na adalci.
[ad_2]
Source link