Abba zai koma jam’iyyar APC a ranar Litinin
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai koma jam’iyyar APC a hukumance ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya fice daga jam’iyyar NNPP.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba tun da farko ya fara shiga APC a shekarar 2014, inda ya lashe zaɓen fidda gwani domin yin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Sai dai daga baya ya haƙura da yin takarar, inda ya bar wa Rabiu Musa Kwankwaso, domin yin takarar.
Bayan shafe shekaru yana siyasa a jam’iyyu daban-daban, ciki har da NNPP, gwamnan ya ce halin da ƙasa ke ciki a yanzu, buƙatar haɗin kan ƙasa da ci gaba ne, suka sa ya yanke shawarar komawa APC.
Gwamnan ya bayyana cewa komawarsa jam’iyyar mai mulki zai ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, ta hanyar samar da ayyukan more rayuwa da ciyar Jihar Kano gaba.
Ya kuma yi fatan matakin zai taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali da haɗin kai da ci gaban siyasa a jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar Litinin, gwamnan zai yi rajista da jam’iyyar APC a Kano tare da ’yan majalisar dokokin jihar 22, ’yan majalisar wakilai takwas, da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Haka kuma ana sa ran gwamnan zai ƙaddamar da rajistar zama ɗan jam’iyyar APC a wannan rana.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link