Gwamnan Taraba ya shiryawa gwamnonin Arewa Maso Gabas liyafa
[ad_1]
Gwamnan Jihar Taraba, Dokta Agbu Kefas, ya shirya wa Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas inda ya shirya musu ƙasaitaccen biki da liyafar dare a Jalingo, a gabanin taron gwamnonin da za a gudanar yau Asabar.
An gudanar da liyafar ne a daren Juma’a a babban ɗakin fadar gwamnati, inda aka nuna raye raye na al’adu daga kungiyoyin gargajiya na Taraba da sauran jihohin yankin.
A jawabinsa, Gwamna Kefas ya bayyana cewa haɗin kan Arewa maso Gabas na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin tsaro, talauci da rashin ingantattun ababen more rayuwa.
Ya kafa da cewa taron gwamnonin na bayar da dama ta musamman don tsara manufofi da inganta zaman lafiya da ci gaban yankin.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun fadar gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya nanata kudirin gwamnonin na yin aiki tare domin ci gaban Arewa maso Gabas baki ɗaya.
Shugaban taron, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jinjinawa Gwamna Kefas bisa shirya wannan liyafa, yana mai cewa baje kolin al’adu da zumunci za su ƙara karfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin jihohin yankin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link