An Damfari Masu Amfani Da Wayar Hannu Naira Biliyan 12.5 A Shekara 4
[ad_1]
Wani sabon bincike daga masana’antar PWC ya bayyana yadda aka damfari masu amfai da wayar hannu naira biliyan 12.5 a Nijeriya a cikin ‘yan shekarun da suka gabata tsakanin 2019 zuwa 2023), ta hanyar karuwar zamba ta intanet.
Wannan asarar kudi ta faru ne a tsakiyar gargadi daga hukumomin da ke kula da tsare-tsare da masana tsaro game da sabon barazanar laifukan intanet da fasahar sadarwa ta zamani (AI) ke haifarwa, wanda ke barazana ga yadda matakan kariya na yanzu ke aiki.
- 2027: Ministocin Da Ake Tsammanin Za Su Yi Murabus Kafin Wa’adin Tinubu Na Ranar 31 ga Maris
- ADC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takara Kafin Babban Taron Jam’iyya
An fayyace wannan a cikin wani sabon bincike na sassa na PwC, wanda ke nuna zurfin matsala a tattalin arzikin zamani na kasar. Duk da cewa sadarwa ta zama ginshiki na ayyukan tattalin arzikin Nijeriya, kayan aikin sadarwar sun zama wurin farautar manyan kungiyoyin masu aikata laifukan zamba.
Asarar da aka ruwaito ta hada da nau’ikan ayyukan laifi, ciki har da yaudaran musayar SIM, ziyarce-ziyarce na ‘phishing’, da zagon-kasa na yin koyi da wani wanda ke amfani da amincewar masu amfani da kudin hannu da ayyukan sadarwa.
A cikin rahoton PwC, kashi 59 cikin dari na masu amfani da bankuna ta intanet a Nijeriya sun fada cikin wannan damfara, wani yanayi da ke nuna cibiyoyin sadarwa na wayar hannu a matsayin muhimmiyar hanyar sadarwa don fadakarwar bankin hannu, sakonnin tabbatarwa, da hanyoyin biyan kudi na zamani a matsayin masu jan hankali ga masu aikata laifi.
Haka kuma, masu ruwa da tsaki suna nuna damuwa a tsarin ayyukan wadannan masu zamba. Don haka, hadewar fasahar sadarwa ta zamani na kawo cikas ga ‘yan damfara na intanet yayin da kuma ke karfafa girman hare-harensu.
Kera muryar da AI ke bayarwa, yin ‘phishing’ da fasahar ‘deepfake’ suna karuwa wajen amfani da kauce wa ka’idojin tsaro wadada aka saba amfani da su, wanda ke sanya wahala ga talakawa su bambanta tsakanin masu ba da sabis na gaskiya da masu aikata mummunan abu.
A halin yanzu, kwararru sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki mataki mai tsauri, suna ba da shawarar kafa hukuma ta musamman ta yakar laifukan intanet wacce za ta hada gwiwa da NCC da kamfanin sadarwar tauraron Dan’adam na Nijeriya (NIGCOMSAT), da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa (ONSA).
Wani babban jami’in kamfanin sadarwa, ya yi magana bisa sharadin rashin bayyana sunansa, ya ce, “Ba ma la’akari da kananan masu sata ba, mun fi mayar da hankali kan kungiyoyin masu tsara ayyukan zambar kudi da suke amfani da fasahar zamani don damfarar ‘yan Nijeriya.”
Ko da yake yanayin fasahar sadarwar zamani tana ci gaba da canzawa, yaki da damfara a bangaren sadarwa ya koma daga kawai kare masu amfani zuwa al’amari na tsaro na tattalin arzikin kasa, tare da hukumomi wanda a yanzu suka fadi-tashi wajen karfafa tsaro a iyakokin kasa daga karuwar laifuka.
[ad_2]
Source link