’Yan sanda sun kama masu bai wa ’yan ta’adda bayanai, sun ƙwato makamai a Filato
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, sun kama wasu da ake zargi da bai wa ’yan bindiga bayanai.
’Yan sandan sun ce waɗanda ake zargin sun amsa cewa suna taimaka wa masu laifi ta hanyar ba su bayanai kan inda za su kai hari da kuma motsin mutane.
A cewar kwamishinan ’yan sandan jihar, Bassey Ewah, an samu nasarar kama su ne bayan samun sahihan bayanai daga wajen jama’a.
Haka kuma, ’yan sanda sun kama wasu da ake zargi da fashi da makami a yankin Langtang na Kudu bayan wani ya kai rahoto.
A yayin aikin, jami’an tsaro sun ƙwato makamai da dama, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47, ƙaramar bindiga da sauran bindigogi da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifuka.
Rundunar ta gode wa jama’a kan haɗin kai, tare da cewa za a gurfanar da dukkanin waɗanda ake zargin a gaban kotu.
Sun kuma tabbatar da cewa za su ci gaba da yaƙi da laifuka da kuma inganta tsaro a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link