Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
[ad_1]
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki matakin gaggawa kan shugaban Amurka, Donald Trump, bayan barazanar da ya yi na kawo hari Nijeriya.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, Sheikh Gumi ya bayyana barazanar Trump a matsayin wulaƙanci ga ikon Nijeriya, yana mai cewa bai dace wata ƙasa mai cikakken ‘yanci ta zama abin tsoratarwa da irin wannan furuci ba. Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta mayar da martani.
“Ga Trump yana barazanar kawo hari ga ƙasa mai ƴanci. Wannan raini ne mai tsanani, amma za mu iya nuna cewa muna da cikakken iko da mutunci a matsayin ƙasa,” in ji Gumi.
Sheikh Gumi ya kuma shawarci gwamnatin Tarayya da ta kira Jakadan Amurka domin neman janye wannan barazana, tare da gargaɗin cewa idan hakan bai faru ba, Nijeriya ta yanke hulɗar diflomasiyya da Amurka.
“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira jakadan Amurka. Idan ba su janye wannan barazana ba, to mu katse hulɗar diflomasiyya da wannan gwamnati mara mutunci,” in ji shi.
[ad_2]
Source link