Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa

[ad_1]



Darajar Naira ta ɗan ƙaru a kasuwanni, bayan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da rage kuɗin ruwa daga kashi 27.5 zuwa kashi 27.

Wannan mataki, a cewar masana tattalin arziƙi, na nufin gwamnati na ƙoƙarin rage matsin tattalin arziƙi da farashin kayayyaki ga ’yan ƙasa.

A ranar Talata, an sayar da dala ɗaya kan Naira 1,487.36 a hukumance, inda hakan ya nuna samun sauyi idan aka kwatanta da Naira 1,488.60 da aka sayar da ita a baya.

Hakazalika, farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya tashi zuwa dala 67.82 a kan kowace ganga ɗaya, abin da ya ƙaru da kashi 0.3 idan aka kwatanta da farashin baya.

Wannan na iya taimaka wa Najeriya, wadda mafi yawan kuɗaɗenta na samuwa ne daga sayar da mai.

Masana sun ce wannan sauyi ba shi da yawa, amma yana nuna cewa ana iya ganin sauƙin matsin tattalin arziƙi idan aka ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakan.

Sai dai har yanzu farashin kayayyaki a kasuwannin cikin gida na ci gaba da hauhawa, lamarin da ke haifar da ƙalubale ga rayuwar talakawa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *