Sarki Sanusi ne zai jagoranci Hawan Sallah — Gwamnatin Kano
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, shi ne zai jagoranci Hawan Sallar Idil-Fitr na wannan shekarar, yayin da ta fitar da tsauraran matakai domin hana ɓarkewar tarzoma a lokacin shagulgulan.
Gwamnatin ta bayyana cewa, wannan shawara wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ita, ta biyo bayan rahotannin sirri ne da ke nuna yunƙurin wasu mutane na tada zaune tsaye a lokacin Sallar.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar ranar Laraba, gwamnatin ta ce tana nan kan bakanta na kiyaye al’adun Kano, amma zaman lafiya da tsaro su ne a gaba.
A cewar sanarwar, Sarki Sanusi zai gudanar da Hawan Idi tun daga filin Sallar Idi na Kofar Mata, ta hanyoyin da aka ware zuwa Gidan Shettima, sannan ya ƙarƙare a Kofar Fatalwa ta fadar Sarki.
Sanarwar ta ƙara da cewa, za a gudanar da Hawan Nasarawa ta wani salo na daban ba tare da jerin gwanon dawakai ba, yayin da aka dakatar da Hawan Daushe da Hawan Fanisau, da Hawan Dorayi a halin yanzu domin tabbatar da tsaron jama’a.
Gwamnatin ta ce an umarci dukkan hukumomin tsaro da su tsananta sanya ido tare da tabbatar da ganin an bi waɗannan dokoki daki-daki kafin sallah, lokacin sallah da kuma bayan shagulgulan.
Haka kuma, ta buƙaci mazauna jihar da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka, sannan su ba hukumomin tsaro haɗin kai, tare da yin gargaɗi kan yaɗa labaran da ba a tantance ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link