Bukukuwan Kirismati Da Sabuwar Shekara: ‘Yansanda Sun Ƙara Tsaurara Tsaro A Kano
[ad_1]
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kara tsaurara matakan tsaro don gudanar da bukukuwan kirismati da na karshen shekara lafiya, inda ta tabbatar wa mazauna jihar samar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
Kwamishinan ‘yansanda, Ibrahim Bakori ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake ganawa da manyan jami’an ‘yansanda domin kammala shirye-shiryen tsaro a lokacin bukukuwan.
- An Kama Mata 2 Bisa Zargin Shigar Da Miyagun Ƙwayoyi Gidan Gyaran Hali Na Kano
- Kogi Poly Ta Sallami Ma’aikata Biyu Kan Cin Zarafin Jima’i Da Rashin Zuwa Aiki
Bakori ya ce, matakan sun yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, inda ya umarci dukkan shugabannin rundunar ‘yansanda na jihohi da su tabbatar da an yi bikin cikin kwanciyar hankali ba tare da aikata laifuka ba a duk fadin kasar.
“Mun kammala cikakken shirye-shiryen tsaro don tabbatar da cewa mazauna Kano sun ji dadin lokacin bukukuwan ba tare da tsoro ba,” in ji kwamishinan.
[ad_2]
Source link