Fintiri da ’yan majalisar dokokin Adamawa 13 na shirin komawa APC
[ad_1]
Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri tare da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Bathiya Wesley, da wasu ’yan majalisa 13 sun fice daga jam’iyyar PDP, inda suke shirin komawa APC.
Majiyoyi sun ce ficewar ’yan majalisar zai taimaka wa gwamnan wajen sauya sheƙarsa cikin sauƙi.
Fintiri ya sha yunƙurin ficewa daga jam’iyyar PDP, musamman bayan saɓanin da ya samu da wasu gwamnonin jam’iyyar a taron ta da aka yi a Ibadan.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kai ziyara jihar kwanan nan domin ƙaddamar da wasu ayyuka, inda rahotanni suka ce sun tattauna batutuwan siyasa da gwamnan.
Abin da sauya sheƙar zai haifar
Idan Fintiri ya sauya sheƙa, zai zamana jam’iyyar APC tana da iko da jihohi kusan 30, yayin da PDP za ta rage da gwamnonin jihohi uku kacal, sauran ƙananan jam’iyyu kuma na ɗaya kowacce.
Kakakin majalisar ya sanar da ficewarsu a zaman majalisar ta yi.
Daga cikin waɗanda suka fice akwai Mataimakin Kakakin Majalisar, Mohammed Buba Jidjiwa, da sauran ’yan majalisa daga mazaɓu daban-daban.
Ɗan majalisa mai wakiltar Lamurde, Bauna Myandiasa, bai halarci zaman ba.
Mataki na gaba
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar, Mahmud Kallamu, ya ce za su tuntuɓi al’ummominsu kafin yanke shawarar jam’iyyar da za su koma.
Ya ƙara da cewa matakin da gwamna Fintiri zai ɗauka ne zai buɗe musu hanyar jam’iyyar da ya dace su koma.
A nasa martanin, mai magana da yawun APC a jihar, Mohammed Abdullahi, ya ce abin da ke faruwa na nuna yadda jam’iyyar ke jan hankalin ’yan siyasa har da ’yan adawa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link