Sin Ta Yi Imanin Karin Kamfanonin Mabambantan Kasashe Za Su Zo Hong Kong Don Zuba Jari Da Fara Kasuwanci
[ad_1]
A ranar 5 ga watan nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian, ya bayyana cewa ya yi imanin karin kamfanoni daga mabambantan kasashe daban daban, ciki har da Amurka, za su zuba jari da fara kasuwanci a Hong Kong, tare da raba cin gajiyar ribar tsarin zamanantarwa na Sin da kuma manufar tsarin “Kasa Daya Amma Tsarin Mulki Biyu.”
An ruwaito cewa, Kungiyar ’Yan Kasuwan Amurka a Hong Kong ta fitar da rahoton shekara ta 2026 mai taken “Rahoton Gamsuwa da Binciken Sha’anin Kasuwancin Hong Kong”, wanda ya nuna cewa kamfanonin Amurka da aka yi bincike a kansu a Hong Kong, suna kara nuna kyakkyawan fata game da yanayin kasuwanci a Hong Kong, tare da cikakken kwarin gwiwa kan makomar ci gabanta.
Lin Jian ya ce, “Rahoton ya nuna cewa kashi 86% na kamfanonin da aka yi bincike kansu suna ganin Hong Kong a matsayin cibiyar kasuwanci ta duniya, kuma ta iya gasa. Kashi 92% na kamfanonin kuma ba su da niyyar dauke hedkwatarsu daga Hong Kong, kuma kashi 94% na kamfanonin suna da kwarin gwiwa kan tsarin doka na Hong Kong.
Wadannan bayanai suna nuna cewa kamfanonin Amurka da ke Hong Kong suna ci gaba da karfafa kwarin gwiwarsu kan makomar ci gaban Hong Kong da yanayin kasuwancinta. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link