Ana Fargabar An Kashe Sama Da Mutum 200 A Harin Kwara
[ad_1]
Ana fargabar sama da mutane 200 sun mutu bayan wasu mahara ɗauke da makamai suka kai hari garin Woro a Karamar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara.
An kuma sace mata da dama, yayin da magidanta da yawa suka tsere daga gidajensu.
- Kwankwaso Bai Je Ƙasar Waje Neman Magani Ba – Kwankwasiyya
- Yadda Fasahar Sin Ke Agaza Wa Samun Wadataccen Hatsi A Afirka
Mazauna yankin sun ce maharan sun isa ne da yammacin ranar Talata, inda suka fara harba bindiga sama kafin su ƙaddamar da mummunan hari na tsawon sa’o’i.
Duk da cewa jirgin saman soji ya tilasta musu ja da baya na ɗan lokaci, sun dawo daga baya cikin dare inda suka ci gaba da kisan gilla.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Da farko harba bindiga sama suka dinga yi. Lokacin da jirgin sojoji ya zo, sai suka ɓuya, amma bayan ya tafi, sai suka dawo suka ci gaba da kashe mutane har zuwa wayewar gari.”
Wasu majiyoyi sun ce an birne gawarwaki sama da 170, yayin da mutane da dama har yanzu ba a gano inda suke ba.
An ƙone gidaje, kuma an gano gawarwaki a cikin gidajen jama’a.
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ziyarci Woro tare da jami’an tsaro, kuma ya tsaya a garin har sai da aka tura ƙarin dakarun soji.
Ya yi Allah-wadai da harin, tare da bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliya ta sojoji domin daƙile ƙarin hare-hare.
Haka kuma, ya umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar da ta tallafa wa waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin.
[ad_2]
Source link