Yadda Fasahar Sin Ke Agaza Wa Samun Wadataccen Hatsi A Afirka

[ad_1]

Kwanan nan, Sin ta fitar da kundinta mai lamba ta farko a shekara ta 2026, wato kundin da ya shafi muhimman manufofin kasar da ta kan bayar a farkon kowace shekara. Abin lura shi ne, takardar ta sanya “fadada amfani da jirage marasa matuki, da tsarin hada mabambantan abubuwa da yanar gizo wato ‘Internet of Things’ da mutum-mutumin inji” a matsayin muhimmin abu wajen zamanantar da aikin noma.

Wannan shi ne karon farko da aka ambata jirage marasa matuki da mutum-mutumin inji a cikin kundin. Bayanai daga ma’aikatar kula da noma da karkara ta Sin sun nuna cewa, yawan jirage marasa matuki da Sin take amfani da su wajen ayyukan noma ya kai fiye da dubu 300, kuma fadin gonakin da wadannan na’urorin ke kulawa a shekara ya wuce hekta miliyan 30.7. Tattalin arziki mai nasaba da zirga-zirgar jiragen sama ko na’urori a kusa da doron kasa yana samun nasarorin a zo a gani a fagen noma, kuma yana nuna alamar ci gaba da habaka.

Wannan ba wai kawai yana bayyana makomar ci gaban kauyuka da karkarar Sin ba ne, har ma da nahiyar Afirka mai nisa tana cin gajiya. Fasahohin noma na zamani ciki har da jirage marasa matuki, suna zama sabuwar hanyar hadin gwiwar noma tsakanin Sin da Afirka.

A karkashin rana mai zafi a lardin Gaza na Mozambique, manomi mai suna Marcus wanda ke da shekaru 58 a duniya ya tsuguna a gefen gonar shinkafa cikin murmushi, yana kallon yadda jirgin sama mara matuki na Sin yake aiki. Wannan jirgi mara matuki na Sin yana aiki ne bisa tsarin ba da jagorancin zirga-zirga na BeiDou na kasar Sin, wanda kuma ke iya fesa maganin kau da ciyayi daidai tsayin mita 3, kuma fadin gonakin da aikin jirgin ya shafa cikin awa 1 har ya fi na wanda shi da dansa suka yi da hannu a cikin kwanaki 3.

Yanzu karin kasashen Afirka suna amfani da tsarin tauraron dan adam mai ba da jagorancin zirga-zirga na BeiDou da na’urorin da ke da alaka da shi, wanda ya zama sabon ginshikin dake ingiza hadin gwiwar noma tsakanin Sin da Afirka. Yanzu, ayyukan hadin gwiwar noma na Sin da Afirka na amfani da jirage marasa matuki a bangarori iri-iri kamar bincike da shata gonaki da shuka shinkafa, da fesa maganin kau da ciyayi, inda fadin gonakin da na’urorin suka yi aiki ya wuce hekta 5333.

Nasarorin da kasar Sin ta cimma ta fannin zamanantar da ayyukan gona, sun kuma biya manyan bukatu guda biyu a harkar noma ta Afirka: Na farko jirage marasa matuki na iya rage rashin tabbas da manoma kan fuskanta sakamakon sauyin yanayi. Na biyu, ba kamar manyan ayyukan gine-gine na baya ba, irin wannan kayan aikin dijital mara nauyi ya fi saukin karbuwa da kuma gudanarwa ga kananan manoma da kamfanonin wurin.

Cikin gomman shekaru da suka wuce, Sin ta karkata daga dogaro da karfin mutum da dabbobi zuwa amfani da injunan noma, har zuwa na’urorin zamani. Abin da Sin ke samarwa ga Afirka, ba wai kawai jirgin mara matuki ba ne, har ma da shigar da sabbin fasahohi cikin tattalin arzikin noma na yankin Afirka da horar da kwararrun fasaha don samun ci gaban noma mai dorewa a wurarensu.

Idan mun yi hangen nesa, hadin gwiwar Sin da Afirka a fagen noma na zamani, ma’anarsa za ta zarce fasaha ita kanta. Lokacin da manoma da kwararrun fasaha na Afirka suka iya amfani da jirage marasa matuki da sauran fasahohi don kara samar da amfanin gona, ma’anarsa ba ta yi kasa da gina wata madatsar ruwa ko babbar hanya ba ce, wanda hakan zai samar da “ginshikan fasaha” wajen samar da isashen abinci da makomar noma a Afirka.(Mai zane da rubutu: MINA)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *