An ceto mutane 8 a rugujewar gini a Abuja
[ad_1]
An ceto mutane takwas daga ƙarƙashin baraguzan wani gini mai hawa uku da ya ruguje a yankin Jikwoyi Phase 1 da ke Abuja, a safiyar ranar Juma’a.
Kwamishinan ’Yan Sandan Birnin Tarayya Abuja, CP Ahmed Mohammed Sanusi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin lokacin da ya jagoranci manema labarai zuwa wurin, ya bayyana cewa rundunar za ta gayyaci dukkan ɗaiɗaikun mutane da hukumomin da ke da alhakin amincewa, ba da lasisin ginin da kuma duba aikin ginin domin yi musu tambayoyi.
Wannan na ɗaya daga cikin ƙoƙarin tabbatar da adalci da kuma kauce wa faruwar hakan a nan gaba.
Ya ce, rundunar ta sami kiran wayar gaggawa ne da misalin karfe 9:00 na safe game da rugujewar ginin mai hawa uku da ake kan ginawa a unguwar Jikwoyi Phase 1.
Kwamishinan ya bayyana cewa, bayan samun rahoton ya tattara jami’ai tare da mataimakin Kwamishinan ’yan sanda (DCP) mai kula da ayyuka da kuma tawagar ceto zuwa wurin.
An gaggauta katange yankin, sannan aka fara gudanar da aikin ceto cikin tsari, tare da tallafin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA), ƙungiyar Red Cross ta Najeriya, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, jami’an gwamnatin birnin tarayya (FCTA) da kuma wakilan kamfanin gine-gine na CGC.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa ma’aikata 17 ne ke kan aiki a lokacin da ginin ya ruguje.
An ceto mutane takwas daga ƙarƙashin baraguzan ginin kuma an garzaya da su asibitin Yan uwa na Asibitin haihuwa da ke Jikwoyi, inda suke karɓar magani a halin yanzu.
Duk da haka, CP Sanusi ya ce ana ci gaba da aikin ceto domin gano ko akwai sauran mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ginin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link