Sin Ta Tsaurara Matakan Fatattakar Haramtattun Harkoki A Sashen Kudi

[ad_1]

Mahukuntan kasar Sin sun kaddamar da wani sabon shiri domin fatattakar haramtattun masu shiga tsakani da ke da hannu a ayyukan da suka saba wa doka ko kuma wadanda ke kan iyakar doka a bangaren kudi, a matsayin wani yunkuri na tabbatar da bin ka’idar doka da kuma kare abokan hulda na harkokin kudi.

Shirin, wanda ma’aikatar tsaron al’umma da kuma hukumar daidaita al’amuran kudi na kasar suke jagoranta, zai mai da hankali ne kan masu shiga tsakani da ke gudanar da haramtacciyar ajiyar kudi da ba da lamuni, da ayyukan ba da bashi ta shafin intanet da ba a amince da su ba, da haramtattun dillalan inshora da sauransu, kamar yadda aka bayyana a wani taro da aka gudanar a jiya Alhamis.

Mahukuntan kasar sun lashi takobin zurfafa bincike kan gungun masu aikata laifuka tare da bin diddigin wadanda ke da hannu dumu-dumu a cikin wadannan aika-aika. Sun kuma yi kira da a inganta harkokin kudi tare da karfafa aiwatar da doka domin kawar da haramtattun ayyukan da ake yi a wannan sashe. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *