‘Yan Nijeriya Miliyan 14.3 Ke Mu’amala Da Muggan Kwayoyi —Gidauniyar Sardauna
[ad_1]
Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello (SABMF) ta bayyana cewa kusan ‘yan Nijeriya miliyan 14.3 suna ta’ammali da miyagun kwayoyi, inda matasa ke daukar babban kaso na wadanda abin ya shafa.
Gidauniyar ta bayyana wannan yanayin abin da ke barazana ga kasa da ke bukatar kulawar gaggawa da daukar mataki daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
- Ba Za A Iya Daidaita Batun Mashigin Hormuz Ba Har Sai An Kawo Karshen Yaki
- Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da ‘Yan Nijeriya 1,231 Daga Jamhuriyar Nijar A Mako Daya
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 30 ga Maris, 2026, bayan shirin kara wa juna sani na wata-wata da gidauniyar ta gudanar ta intanet, inda aka tattauna tasirin illar ta’ammuli da miyagun kwayoyi a zamantakewa da tattalin arziki.
Mai gabatarwa, Dakta Muhammad Kasim na asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) ya kawo bayanai daga ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan miyagun kwayoyi da aikata laifuka, wanda ke nuna cewa Nijeriya tana da kashi 14.4 cikin dari na yawan amfani da miyagun kwayoyi, wanda ke nuna cewa kusan masu mutum miliyan 14.3 ke ta’ammuli da miyagun kwayoyi a fadin kasar.
A cewar gidauniyar, yawan amfani da miyagun kwayoyi tsakanin matasa yana haifar da babban hadari ga ci gaban kasa da lafiyar jama’a, da kuma tsaro.
Ta kara da cewa karuwar amfani da kwayoyi na gargajiya da na asibiti na haifar da karin yawan shaye-shaye, rashin lafiyar kwakwalwa, da matsin lamba ga tsarin kiwon lafiya.
Gidauniyar ta kuma yi gargadin cewa wannan yanayin yana taimakawa wajen raguwar samarwa da karuwar laifuka, da lalacewar tsarin iyali da karuwar matsalolin ilimi.
SABMF ta nuna damuwa musamman a arewacin Nijeriya, inda talauci da rashin aikin yi da karancin shiga makaranta, da yawan yara da ba su zuwa makaranta ke kara sa matasa su kasance cikin hadarin shan miyagun kwayoyi.
[ad_2]
Source link