Sin: A Bari Jama’ar Kasar Iran Su Daidaita Harkokinsu Na Cikin Gida
[ad_1]
A jiya Juma’a, kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, ya gudanar da wani taron musamman, don tantance yanayin da kasar Iran ke ciki, a fannin hakkin bil Adama. Inda jakadan kasar Sin a ofishin MDDr dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland, Mista Jia Guide, ya bayyana ra’ayin kasar Sin game da batun, yana mai cewa duk wata kasa tana da ‘yancin zabar hanyar da take so don tabbatar da hakkin dan Adam.
Ya ce kasar Sin tana adawa da matakan tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, da fakewa da maganar hakkin dan Adam, da tantance yanayin hakkin dan Adam na kasashe daban daban ba tare da neman izini daga wajensu ba, da raba kafa dangane da batun kare hakkin bil Adama.
Jami’in na kasar Sin ya kara da cewa, al’amarin dake faruwa a Iran batun cikin gidan kasar ne, don haka ya kamata a bari jama’ar kasar su yanke shawara da kansu. Ya ce kasar Sin har kullum tana kira da a bi ka’idojin MDD da dokokin kasa da kasa, da kin amincewa da daukar matakan soja, ko barazanar yin hakan, yayin da ake hulda da sauran kasashe, da adawa da mulkin danniya.
Jia Guide ya kara da cewa, kamata ya yi gamayyar kasa da kasa su girmama ikon kasar Iran na mulkin kai, da tabbatar da tsaron kasa, da hurumin yankunanta, da samar da taimako ga gwamnatin Iran da jama’arta, ta yadda za su iya kiyaye kwanciyar hankali, da kare hakkin kasar bisa adalci. Kana a nata bangare, kasar Sin na son ganin bangarori masu ruwa da tsaki, sun daidaita bambance-bambance ta hanyar shawarwari, inda bangaren Sin ke son samar da nasa taimako.
A wadannan kwanaki, yanayin siyasa da kasar Iran ke ciki, na janyo hankalin mutanen duniya. Daga bisani kasar Iceland, da sauran kasashe, sun bukaci kwamitin hakkin dan Adam na MDD, da ya kira taron musamman don kara nazartar wannan batu. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link