Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 9 A Wurin Shaƙatawa A Filato

[ad_1]

Aƙalla mutane tara sun rasa rayukansu bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai a wani wurin shaƙatawa a ƙauyen Doruwa Babuje, ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato. Harin ya faru da misalin ƙarfe 7:15 na yammacin Lahadi, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici.

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun kutsa cikin wurin tare da buɗe wuta ba tare da bambanci ba kafin su tsere. Wasu mutum biyu sun samu munanan raunuka kuma ana kula da su a wani asibiti da ke kusa.

  • Gwamnan Kano Ya Sauke Buba Galadima Daga Muƙamin Shugaban Gudanarwar Kano Poly
  • Tinubu Bai Shirya Yin Gaskiya A Zaɓen 2027 —Buba Galadima

Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar matasan Berom, Rwang Tengwong, ya bayyana harin a matsayin abin takaici da girgiza zuciya, yana mai cewa ya yi matuƙar shafar al’ummar yankin.

Kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Captain Chinonso Oteh, ya ce sojoji sun kai ɗauki cikin gaggawa bayan samun kiran gaggawa. Ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike tare da ƙarfafa tsaro a yankin, yayin da ake farautar waɗanda suka aikata harin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *