Kwaccham ya gindaya sharaɗi ga Gwamna Fintiri kan rade-radin komawarsa APC
[ad_1]
Wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham ya gindaya wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri sharaɗi la’akari da jita-jitar da ake yaɗawa na shirin ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Gwamna Fintiri wanda ke kan wa’adinsa na biyu a mulkin jihar, na cikin gwamnoni uku kaɗai da suka rage a jam’iyyar adawa daga yankin Arewa, ragowar biyun su ne Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Bala Muhammad Abdulkadir, sai kuma Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara.
A yayin da yawancin gwamnonin da ke komawa jam’iyyar APC ke danganta matakin nasu da matsalar rigingimu a jam’iyyar su, sai kuma yunƙurin shawo kan Gwamnatin Tarayya kan samar da ƙarin ayyukan ci gaba a jihohinsu, akwai zargin cewa a ɗaya ɓangaren, gwamnoni da ke kan wa’adi na biyu na ɗaukan matakin ne kan fargabar fuskantar shari’a da zaran sun rasa kariya da suke da ita, a ƙarshen wa’adin mulkin su.
Da yake zantawa da wasu manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, Alhaji Abdurrahman Kwaccham wanda har ila yau shi ne, Sarkin Fulani na Masarautar Mubi da ke Jihar Adamawa, ya ce “idan har zargin komawar gwamnan jiharmu zuwa jam’iyyarmu ya tabbata, to abin marhabin ne.”
Sai dai a cewarsa “ya kamata Gwamnan ya kwana da sanin cewa ɗaukar matakin ba zai ba shi lasisin zama jagoran jam’iyyar APC a jihar ba, koda ya koma cikinta.
“Saboda haka ina gargaɗin shugabannin jam’iyyarmu ta APC a matakin ƙasa da su kiyayi ɗaukan irin wannan matakin a Jihar Adamawa, saboda hakan na iya hargitsa jam’iyyar.
“Ina wannan kashedin ne saboda kafa hujja da ake yi da cewa tsari da ƙa’idojin jam’iyyarmu sun bai wa duk wani gwamna mai ci da ya koma cikinta, damar zama shugabanta.
“To ya kamata su san da cewa, ƙarfin mulki kaɗai bai samar da nasara a Jihar Adamawa, kamar yadda ta kasance ga tsohon gwamnan jihar, Muhammad Bindow Jibrilla da ya sha kaye a lokacin da yake gwamna duk da kasancewa jam’iyyar ce ke da shugaban ƙasa, wato marigayi Muhammadu Buhari.
“Sannan har ila yau, jam’iyyar ta sake shan kaye, inda ’yan takarararta a zaɓen gwamnan jihar, wato Sanata Aishatu Binani ta faɗi a zaɓen da ya biyo baya, a hannun gwamnan jihar na yanzu Ahmadu Fintiri.
“Irin hakan ne ya kasance a Jihar Zamfara inda gwamnan jihar mai ci Bello Matawalle ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar adawa da ke mulkin jihar a yanzu wato Gwamna Dauda Lawal, a dalilin an ƙwace ragamar jam’iyyar APC daga hannun mai yi mata hidima wato Sanata Abdulaziz Yari.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link