Jerin ministocin da zargin takardu ya tabaibaye suna ofis

[ad_1]



A yayin Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, Uche Nnaji, ke fuskantar matsin lamba bayan ya amsa a gaban kotu cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba, zargin sa da amfani da takardun bogi da kafar PREMIUM TIMES ta bankaɗo ya ƙara ƙarfi.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce za ta jira hukuncin kotu kafin ta ɗauki mataki kan batun Nnaji.

Wannan ya sanya Mista Nnaji cikin jerin wasu ministoci da suka fuskanci irin wannan tuhuma:

– isarwa

Uche Nnaji, wanda Shugaba Bola Tinubu ya nada a watan Yuli 2023, ya gabatar da takardar digiri da kuma takardar kammala aikin NYSC a lokacin tantancewa. Amma jami’ar UNN da hukumar NYSC sun ce ba su da masaniya da takardun da aka gabatar.

Shugaban jami’ar UNN, Farfesa Simon Ortuanya, ya tabbatar cewa an ɗauki Nnaji karatu a 1981 amma bai kammala ba.

NYSC ma ta ce takardar da Nnaji ke amfani da ita ba ta da tushe.

– Kyautar Gungeon

Ministan Cikin Gida, an zarge shi da gabatar da takardar NYSC ta bogi.

Amma daga bisani NYSC ta ce takardarsa ta gaskiya ce, bayan an sake tura shi aikin a 2019.

– Stella Oduah:

Taohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama, an zarge ta da ƙin kammala aikin NYSC a 1982.

A 2023, EFCC ta gurfanar da ita bisa zargin jabun takardu da bayanan ƙarya. Ta musanta zargin, kuma shari’ar na gaban kotu.

– Hannatu Musawa

Saɓanin Nnaji da Olubumi da ake zargi da amfani da takardun bogi, da Stella Oduah da ke zargi da ƙin kammala aiki NYSC, qn yi zargin cewa Ministar Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙre-ƙirƙiye, tana cikin aikin NYSC lokacin da aka naɗa ta a 2023.

Ministar ta ci gaba da kare kanta cewa ba ta aikata laifi ba, kuma ta kammala aikin NYSC.

Kotun tarayya ta yi watsi da ƙarar da aka shigar, duk da tambayoyi da ke ci gaba da tasowa.

– Adebayo Shittu:

Tsohon Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu kuma, an zarge shi ne kan ƙin halartar aikin NYSC kasancewar ya kammala jami’a ne a lokacin da yake ɗan shekara 25.

Amma ya bayyana cewa zaɓen sa da aka yi a matsayin ɗan Majalisar Dokokin Jihar Oyo ya maye gurbin aikin, amma NYSC ta ce ba haka doka ta tanada ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *