An tsare wani mutum kan yi wa Gwamnan Neja ihun ‘ba ruwa, ba wuta’
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da kama wani mutum mai shekaru 38, Hamisu Abdullahi, kan yi Gwamna Mohammed Umaru Bago ihun “ba ruwa, ba wuta”.
Rahotanni sun nuna cewar lamarin ya farj ne lokacin da Gwamnan ya kai wa Sarkin Suleja ziyara bayan idar da sallar Idi ƙarama a ranar Juma’a.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.
Ya ce an kama mutumin ne bisa zargin ƙoƙarin tayar da tarzoma yayin ziyarar gwamnan.
Ya ce, “Wani Hamisu Abdullahi, mai shekaru 38, ɗan Suleja, an kama shi kuma an miƙa shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Minna, a ranar 20 ga Maris, 2026, bisa zargin ƙoƙarin kawo cikas ga harkokin gwamnati yayin ziyarar Sallah.”
Ya ƙara da cewa, “Sai dai daga baya an bayar da belinsa yayin da ake ci gaba da bincike.”
Ɗan uwan Hamisu, Haruna Abdullahi, ya kuma tabbatar da cewa an sake shi da yammacin ranar Talata bayan ya shafe kwanaki biyar a hannun ’yan sanda.
Hamisu, magidanci ne mai ’ya’ya huɗu kuma yana zaune a Unguwar Bayi da ke Suleja.
An ce an kama shi ne bayan ya yi ihun a fadar Sarkin yayin ziyarar gwamnan.
A gefe kuma kuma, ana raɗe-raɗin cewa an kama shi ne bisa umarnin gwamnan, amma kawo yanzu babu tabbaci game da hakan.
Da aka tuntuɓi Sakataren Yaɗa Labaran gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce ba shi da masaniya kan lamarin.
Ita kuwa, Cibiyar International Press Institute (IPI) Nigeria, a ranar Litinin ta buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gargaɗi Gwamna Bago kan duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga ’yancin aikin jarida a jihar.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Shugabanta, Fidelis Mbah, da mai ba ta shawara kan harkokin shari’a, Tobi Soniyi, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce wasu matakai da gwamnan da jami’ansa suke ɗauka suna shafar ’yancin ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai wajen gudanar da aikinsu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link