Ba mu da alaƙa da kyautar mota da shago da aka yi wa Rahama Sa’idu — Gwamnatin Sakkwato
[ad_1]
Gwamnatin Sakkwato ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da kyautar mota da kuma shago da wani mutum mai suna Sani Jaman ya bai wa wata ’yar TikTok, Rahama Sa’idu, ’yar asalin Jihar Kebbi.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ofishin Mai Magana da Yawun Gwamnan Sakkwato ya fitar, wadda Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Abubakar Bawa, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce ofishin ya ja hankalinsa ne kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna Sani Jaman yana bai wa Rahama Sa’idu mota ƙirar KIA, wadda ake hasashen kuɗinta ya kai kusan naira miliyan tara, tare da shago, inda aka danganta kyautar da Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto.
A cewar sanarwar, Sani Jaman ya yi iƙirarin ya bayar da kyautar ce bisa ra’ayinsa na ƙashin kai, sakamakon irin goyon baya da ƙaunar da Rahama Sa’idu ke nuna wa gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu, ba tare da wani umarni ko sani daga ɓangaren gwamnatin jihar ba.
“Don kau da duk wani ruɗani, muna so mu bayyana a ƙarara cewa wannan kyauta ba ta da wata alaƙa da Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto ko Gwamnatin Jihar Sakkwato. Lamari ne na ƙashin kai tsakanin wanda ya bayar da kyautar da wadda aka ba,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma yi tir da irin wannan aiki, tare da gargaɗin mutane da su daina yin duk wani abu a sunan Gwamna ko Gwamnatin Jihar Sakkwato ba tare da sahalewar hukumomin da suka dace ba.
Gwamnatin ta jaddada cewa tana maraba da tallafi daga masu hannu da shuni da sauran ’yan kasa masu kishin jihar, amma ta ce ya dace a riƙa bayar da irin wannan tallafi ta hanyoyin da suka dace, tare da la’akari da muradun al’umma baki ɗaya.
A cewar sanarwar, gwamnatin Ahmed Aliyu na aiwatar da manufofinta na Ajandar Maki Tara (9-Point Smart Agenda), wadda ta haɗa da yaƙi da rashin tsaro, tarbiyya da gyaran halayen jama’a, tallafa wa marasa galihu da suka hada da marayu, zawarawa da masu nakasa, ƙarfafa matasa, tsaftar muhalli, bunƙasa ilimi, da kuma inganta harkokin lafiya.
Sanarwar ta ƙara da cewa har yanzu akwai ɗimbin ’yan gudun hijira, musamman a yankunan da hare-haren ’yan bindiga suka shafa, har ma a cikin babban birnin jihar, waɗanda ke buƙatar taimako matuƙa.
“Duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi wajen tallafa wa waɗannan rukunoni, har yanzu akwai buƙatar ƙarin gudummawa daga attajirai da kamfanoni domin rage raɗaɗin da jama’a ke ciki,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta yi kira ga masu hali da su haɗa kai da ita wajen inganta jin daɗin rayuwa da walwalar al’umma, musamman rukunonin jama’a masu rauni.
Kyautar dai ta haifar da cece-kuce a Jihar Sakkwato, musamman a tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC, inda wasu ke ganin an yi amfani da sunan Gwamna wajen abin da ba shi da alaƙa da harkar kamfe ko wani zaɓe da zai sa a danganta kyautar da Gwamna.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link