Xi Jinping Ya Taya Kim Jong Un Murna Bisa Zabensa Da Aka Yi A Matsayin Sakatare Janar Na Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa
[ad_1]
A yau Litinin, sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ya taya Kim Jong Un murna bisa zabensa da aka yi a matsayin sakatare janar na jam’iyyar WPK ta kasar Koriya ta Arewa.
Cikin sakonsa na taya murna, Xi Jinping ya ce tun bayan babban taro na 8 na WPK, kwamitin tsakiya na jam’iyyar karkashin Kim Jong Un ya hada kan jama’ar kasar tare da jagorantarsu bisa aiki tukuru, inda ya ci gaba da samun sabbin nasarori wajen gina tsarin gurguzu a kasar.
Ya ce sake zaben Kim a matsayin sakatare janar na jam’iyyar WPK ya kara nuna irin aminci da goyon bayan da jam’iyya da gwamnati da al’ummar kasar ke ba shi.
Xi Jinping ya kara da cewa, Sin da Koriya ta Arewa abokai ne makwabta ’yan gurguzu, wadanda suka marawa juna baya tare da taimakawa juna. Ya ce ci gaba da rayawa da karfafa dangantakar Sin da Koriya ta Arewa, manufa ce ta JKS da gwamnatin kasar da ba za ta sauya ba.
Shugaba Xi ya ce a shekarun baya bayan nan, ya hadu da Kim Jong Un sau da dama, lamarin da ya jagoranci raya dangantakar kasashen biyu. Ya kara da cewa, yayin ake samun manyan sauye-sauye cikin sauri irin wadanda ba a taba gani ba cikin karni guda, da hargitsi mai sarkakiya da duniya ke fuskanta, a shirye yake ya hada hannu da Kim Jong Un wajen jagorantar sassa masu ruwa da tsaki da yankunan bangarorin biyu wajen aiwatar da muhimmiyar matsayar da suka cimma, da rubuta sabon babi a abotar Sin da Koriya ta Arewa, da hidimtawa ginuwar burin gurguzu na kasashen biyu, da inganta walwala da abotar al’ummun kasashen biyu, da bayar da kyakkyawar gudunmuwa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba da wadata a shiyyarsu da ma duniya. (FMM)
[ad_2]
Source link