Sin Da Canada Sun Shirya Aiki Tare Domin Samun Sabbin Ci Gaba
[ad_1]
Kasashen Sin da Canada sun shirya karfafa hadin gwiwarsu a fannonin da suka shafi makamashi mai tsafta da fasahar zamani da aikin gona na zamani da harkokin sararin samaniya da kere-kere na zamani da hada-hadar kudi domin ingiza ci gaban tattalin arzikinsu.
An cimma hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi yau Alhamis tsakanin firaministan Sin Li Qiang da takwaransa na Canada Mark Carney, a birnin Beijing.
A cewar Li Qiang, kasar Sin na maraba da kamfanonin Canada su zuba jari a kasar da fatan cewa Canada za ta samar da kyakkyawan muhalli ba tare da nuna wariya ba ga kamfanonin Sin dake zuba jari a kasar.
Bayan tattaunawar, Li da Carney sun shaida rattaba hannu kan daftarorin hadin gwiwa tsakanin kasashensu, wadanda suka shafi cinikayya da harkokin kwastam da makamashi da gine-gine da al’adu da tsaron al’umma. (FMM)
[ad_2]
Source link