Tanka ta kife yayin da man fetur ya zube a kan titi a Neja
[ad_1]
Wata tanka ɗauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lambata zuwa Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja, lamarin da ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin.
An gano cewa tankar, wadda ta taso daga Legas tana kan hanyarta na zuwa Kano, ta kife ne da sassafe a garin Takalafiya da ke Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja.
Wani mazaunin garin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya shaida wa Aminiya cews lamarin ya faru kimanin kilomita biyu daga garin Lapai.
Ya ce kwanan nan aka gyara hanyar NNPCL, amma hanyar ta fara lalacewa cikin ƙanƙanin lokaci.
Wani ganau mai suna Mohammed Hassan Sonmaji ya ce, saurin zuwan jami’an kashe gobara na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBUL) tare da na Hukumar Tsaro ta NSCDC ne ya taimaka wajen kauce wa mummunan hatsari a hanyar.
Ya ƙara da cewa jami’an ƙungiyar NUPENG reshen Lapai, sun isa waje don taimakawa wajen shawo kan lamarin.
An zagaye wani ɓangare da man ya zube domin gujewa aukuwar hatsari.
Da aka tuntubi Daraktan Sashen Bayani da Harkoki na Musamman na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dokta Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da cewa babu abin zai auku.
Ya bayyana cewa tankar ba ta kama da wuta ba, kuma motocin kashe gobara na jami’ar IBBUL suna tsaye a wajen don shirin ko-ta-kwana.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link