UEFA ta dakatar da Prestianni kan nuna wa Vinicius wariyar launin fata

[ad_1]



Hukumar Ƙwallon Ƙafar Turai, UEFA, ta dakatar da ɗan wasan tsakiya na Benfica, Gianluca Prestianni, daga wasa ɗaya na je ka gyara hali, sakamakon zargin yi wa Vinicius Junior kalaman wariyar launin fata.

Dakatarwar, wadda aka ayyana a ranar Litinin, za ta hana Prestianni buga wasan zagaye na biyu da za a fafata a filin Santiago Bernabeu ranar Laraba.

Wannan mataki na wucin gadi ya biyo bayan zargin da ɗan wasan Real Madrid, Vinicius Junior ya yi, inda ya kai rahoto ga alƙalin wasa bayan ya ci ƙwallo a wasan farko da Real Madrid ta yi nasara da 1-0 a Portugal.

UEFA ta ce dakatarwar wasa ɗaya ce ta wucin gadi, kuma ba ta rufe ƙofar ɗaukar ƙarin matakai ba idan bincike ya tabbatar da zargin.

Haka kuma, hukumar ta ce idan aka same shi da laifi, Prestianni mai shekaru 20 na iya fuskantar dakatarwa har na wasanni 10 ko fiye.

Rahotanni sun nuna cewa Vinicius ya kai ƙorafi ne bayan wata muhawara da ta ɓarke tsakaninsa da Prestianni, lamarin da ya sa aka dakatar da wasan na kusan mintuna 10.

Sai dai Prestianni ya musanta zargin, yana mai cewa bai yi amfani da kalaman wariya ba.

Wasu ‘yan wasan Real Madrid sun soki lamarin, inda suka bayyana shi a matsayin abin kunya ga ƙwallon ƙafa.

Ana sa ran hukuncin ƙarshe daga UEFA bayan kammala bincike, yayin da Real Madrid da Benfica ke shirin fafatawa a wasan na biyu domin neman tikitin shiga zagaye na gaba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *