Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen

[ad_1]



Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da ke Sipaniya na ƙoƙarin ɗauko Victor Osimhen a matsayin wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski wanda ke fama da matsalar raunuka

Ɗan jaridar ƙasar Sifaniya, Gabriel Sans na Mundo Deportivo ya bayyana cewar, Barcelona na neman wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski a matsayin mai jefa ƙwallo a raga, hakan ne ya sa ƙungiyyar ta amince da ɗaukar Osimhen.

A ƙarshen kakar bana ne ake tunanin up Lewandowski zai bar Barca, wanda zai tilasta wa ƙungiyyar neman wani zaƙaƙurin ɗan wasan gaba mai ciyo ƙwallo.

Victor Osimhen dai a bazarar nan ne ya koma Galatasaray bayan barin Napoli ta Italiya.

Osimhen dai ba ya ɓoye aniyarsa ta buga wasa a ɗaya daga cikin manyan gasannin Nahiyyar Turai biyar ba, ciki har da Firimiya ta Ingila da LaLiga ta Sifaniya, inda Barcelona ke cikin manyan ƙungiyoyin gasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *