Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC
[ad_1]
A wasan farko na gasar cin kofin ƙwallon yashi wato Beach Soccer da aka fara gudanarwa yau Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, Kada BSC ta lallasa Kebbi BSC da ci 8 – 5.
Kada ta samu nasarar zura ƙwallayen ne ta hannun Frank Dozievda da ya zura 4 a raga, sai Sani Hassan 2, sai kuma Hammed Kareem shi ma da ya zura ƙwallaye 2 a raga.
A ɓangaren Kebbi United kuwa ‘yan wasan na biyar ne kowanne ya zura ƙwallo a raga da suka haɗa da: Isyaku Atiku da Ibrahim Malami da Sadik Umar da Abdullahi Aliyu da Usman Bello.
An karrama ɗan wasa Frank Dozie na Kada BSC saboda bajintar da ya nuna a wasan.
Wasa na gaba da misalin ƙarfe 4:15 na yamma
Kebbi United BSC zata kece raini da Jigawa Golden Stars BSC sai kuma ƙarfe 5:15 inda Kebbi Fishers zata fafata da Anambra Warriors a filin wasa na Jabi Lake Park da ke Abuja.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link