Sinner da Alcaraz za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu

[ad_1]



Carlos Alcaraz da Jannik Sinner za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu a watan Janairu, kwanaki takwas kacal kafin fara gasar Australian Open.

’Yan wasan biyu kuma za su hadu a babban wasan Hyundai Card Super Match a Incheon, a ranar 10 ga Janairu, yayin da za a fara babbar gasar Australian Open a Melbourne a ranar 18 ga Janairu.

Kafin hakan dai ’yan wasan biyu, wadanda suka hadu a wasanni uku daga cikin hudu na Grand Slam a shekarar 2025, sun lashe kofuna tara cikin manyan gasa 10 da suka gabata a tsakaninsu.

Sinner ya dawo a matsayinsa na lamba daya a duniya bayan doke Alcaraz a ranar Lahadi, bayan nasarar maki 6-4 7-6 da ya samu kan Felix a gasar Paris Masters.

Kawo yanzu dai Alcaraz ne ke kan gaba a fafatawar da suka fuskanci junansu, inda ya samu nasara sau 10, yayin da Sinner ya samu nasara sau biyar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *