Genoa ta naɗa Daniele De Rossi sabon kociya
[ad_1]
Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin wannan ranar. Za a gudanar da taron manema labarai na farko da shi a ranar Juma’a.”
De Rossi, wanda ya taka leda na tsawon shekaru 17 a Roma kuma ya lashe Kofin Duniya tare da Italiya a 2006, ya taɓa horas da ƙungiyoyin Spal da Roma.
Roma ce ƙungiyar da De Rossi ya kai zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar Europa League ta 2024, kafin a sallame shi bayan rashin nasara a wasanni hudu a jere a kakar da ta biyo baya.
A makon da ya gabata, Genoa ta kuma sallami daraktan wasanninta Marco Ottolini, inda ta maye gurbinsa da ɗan ƙasar Sifaniya, Diego Lopez.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link