An ci tarar Remo Stars miliyan 7 da haramta musu wasanni
[ad_1]
Hukumar da ke shirya gasar Firimiyyar Nijeriya NPFL ta hukunta ƙungiyar ƙwallon kafa ta Remo Stars sakamakon aikata laifuka da dama a wasan da suka buga da Ikorodu City.
Laifukan sun haɗa da rashin samar da isasshen tsaro, jifan abokanan karawa cikin filin wasa da kuma sauran ɗabi’u marasa kyau daga magoya bayanta.
A cewar Hukumar, ƙungiyar za ta biya tarar Naira miliyan 2 saboda rashin samar da ingantaccen tsaro da kuma ƙarin Naira miliyan 1 saboda jifa a cikin fili.
Haka zalika, Remo Stars za ta biya Naira miliyan 1 sakamakon rashin ɗa’ar da magoya bayanta suka nuna, tare da wata Naira miliyan 1, saboda kawo hargitsi a wasa
An kuma ɗora wa ƙungiyar ƙarin tarar Naira miliyan 2 a matsayin kuɗin diyya na varnar da aka yi wa motar Ikorodu City, tare da haramta musu buga wasanni 4 a gida.
Kawo yanzu dai Remo Stars tana da sa’o’i 48 don ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link