Sojoji sun daƙile hari, sun kashe kwamandojin Boko Haram 2 a Borno

[ad_1]



Sojojin Operation Haɗin Kai sun daƙile wani harin kwanton-ɓauna da mayaƙan Boko Haram suka kai, inda suka kashe ’yan ta’adda da dama ciki har da manyan kwamandojinsu biyu a Jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Janairu, 2026, a yankunan Sambisa da tsaunukan Mandara.

A cewar rundunar sojin, ’yan ta’addan sun yi yunƙurin kai hari ta hanyar dasa bam a gefen hanya.

Amma sojojin sun daƙile yunƙurin nasu tare da nasarar fatattakar su.

Aƙalla ’yan ta’adda 10 ne suka mutu, ciki har da kwamandoji biyu; Basulhu da Ubaida.

Sojojin sun kuma ƙwato makamai, babura, na’urorin sadarwa, gurneti da kayan haɗa bam.

Haka kuma, sojojin sun hana wasu ’yan ta’adda shigowa Najeriya daga ƙasar Kamaru ta yankin Galakura, inda suka tilasta musu komawa.

Rundunar sojin ta ce duk da asarar da ta yi a wasu hare-hare a baya, ta ce za ta ci gaba da yaƙi da ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *