Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool
[ad_1]
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan.
A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila.
Forest ta samu nasarar ce ta hannun Murillo a minti na 33, sai Nicolo Savona a minti na 46, sannan Morgan Gibbs-White ya ƙara na uku a minti na 78.
Sakamakon wannan rashin nasarar, Liverpool ta sauka zuwa mataki na 11 da maki 18, yayin da ita kuwa Nottingham Forest ta matsa zuwa mataki na 16 da maki 12 a teburin gasar.
Kawo yanzu dai, cikin wasanni 12 da Liverpool ta buga a gasar Firimiya, ta samu nasara a wasanni 6 ne kaɗai, sannan an doke ta a sauran 6.
Wannan mummunar rashin nasara ta sake dagula wa mai horar da ƙungiyar, Arne Slot, al’amura, musamman ganin irin matsin lambar da yake fuskanta daga magoya bayan ƙungiyar a bana.
A yanzu, hankalin mai horarwar ya koma kan wasan Champions League da za su yi da PSV a ranar Laraba.
Samun nasara a wannan wasa na iya zama abin da zai ba shi damar sauƙin numfasawa; akasin haka kuma, na iya haifar masa da babbar matsala daga mahukuntan kulob ɗin da magoya bayan da ke ƙara nuna rashin haƙuri.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link