El-Rufa’i Ya Kafa Tubalin Tsaro Da Ilimi A Jihar Kaduna – Jafaru Sani

[ad_1]

Tsohon Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi ta Jihar Kaduna, Malam Jafaru Ibrahim Sani, ya bayyana cewa babu shakka tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, ya kafa tarihi wajen samar da tsaro da kuma bunƙasa harkokin ilimi a lokacin da yake jagorantar al’amuran jihar.

Malam Jafaru ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakilinmu jim kaɗan bayan kammala wani taron jam’iyyar haɗaka ta adawa ta ADC da aka gudanar a birnin Kaduna. A cewarsa, gwamnatin El-Rufa’i ta taka muhimmiyar rawa wajen rage ayyukan ta’addanci da fashi da makami da ƙwacen waya da suka addabi al’ummar jihar a baya.

  • Sace Masu Ibada: Ashiru Ya Caccaki Gwamnatin Kaduna Kan Rashin Iya Shugabanci
  • Sace Masu Ibada: Ashiru Ya Caccaki Gwamnatin Kaduna Kan Rashin Iya Shugabanci

Ya ƙara da cewa a lokacin mulkin El-Rufa’i, an samu gagarumin sauƙi a hare-haren ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a sassa daban-daban na jihar, lamarin da ya bai wa gwamnati damar aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa ba tare da tangarɗa ba. Ya ce wannan sauƙin tsaro ne ya taimaka wajen bunƙasa ayyukan ci gaba a fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da harkokin ƙananan hukumomi.

Tsohon kwamishinan ya ƙara da cewa vangaren ilimi ya amfana matuƙa a lokacin gwamnatin El-Rufa’i, inda aka gina makarantu, aka inganta tsarin koyarwa tare da ɗaukar malamai masu ƙwarewa domin ceto harkar ilimi daga halin da yake ciki.

Haka kuma, ya ce waɗannan matakai sun taimaka wajen farfaɗo da darajar ilimi a Jihar Kaduna tare da samar da kyakkyawan tushe ga ci gaban matasa.

A ƙarshe, Malam Jafaru ya jaddada cewa Jihar Kaduna na buƙatar shugabanci nagari, tsari mai kyau da jajircewa domin dawo da zaman lafiya da ci gaban da al’umma ke fata, yana mai bayyana cewa hakan ne kaɗai zai tabbatar da makoma mai kyau ga jihar da ‘ya’yanta.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *