Gwamnatin Jigawa Ta Lalata Kwalaye 5,520 Na Taliyar Yara Da Lokacin Ingancinta Ya Ƙare
[ad_1]
Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Jigawa (JSPHCDA), tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta lalata kwalaye 5,520 na taliyar yara da lokacin amfaninta ya ƙare, wacce aka shirya rabata ga ƙananan yara don ƙarfafa gwiwarsu wajen yin rigakafi a Jihar.
Jami’in kula da ɓangaren na Jihar, Yusuf Inuwa, ya bayyana hakan a lokacin aikin lalata taliyar, yana mai bayanin cewa, WHO ce ta samar da taliyar don tallafawa ayyukan rigakafin cutar shan inna da aka tsara a watan Nuwamban 2025.
“An yi shirin rarraba taliyar ne a lokacin kwanakin yin rigakafi a jihar (NIPDs),” in ji Inuwa.
Hukumar Kula da Lafiya ta Farko ta Kasa (NPHCDA) ce ta bayar da umarnin a ɗage aikin zuwa ranar 2 ga Disamba, 2025 a maimakon yadda aka tsara tun farko, wanda hakan ya haifar da lalacewar taliyar.
[ad_2]
Source link