Sojoji sun dakile harin ’yan bindiga a kauyukan Kano
[ad_1]
Dakarun rundunar haɗin gwiwa (JTF) sun yi nasarar dakile yunkurin ’yan bindiga na kai hari kan wasu kauyukan ƙaramar hukumar Shanono ta Jihar Kano bayan doguwar musayar wuta.
Arangamar ta fara ne da yammacin Alhamis kuma ta ci gaba har zuwa safiyar Juma’a, a Yankwada, Babanduhu da wasu ƙauyuka makwabta.
Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya a Kano, Manjo Zubair Babatunde, ya tabbatar da lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), inda ya ce ’yan bindigar sun yi ƙoƙarin kai harin ne kan al’ummomin a kan babura suka yi ta harbi ba kakkautawa.
Babatunde ya ce harin na ramuwar gayya ne bayan rasa wasu daga cikin ’yan bindigar a hannun sojoji yayin fafatawa a makon da ya gabata.
A cewarsa, maharan sun kutsa ƙauyukan da abin ya shafa da misalin ƙarfe 1:00 na dare, lamarin da ya sa sojoji suka yi gaggawar mayar da martani.
“An yi nasarar fatattakar ’yan bindigar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa saurin shiga Tsakani da JTF ta yi ya hana aukuwar asarar rayuka da ta dukiya a al’ummomin da abin ya shafa. Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa sojoji za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira gare su da su ci gaba da ba da bayanai cikin lokaci da gaskiya ga hukumomin tsaro.
Mai magana da yawun sojojin ya ce rundunar tana cikin shirin ko-ta-kwana don hana hare-hare a nan gaba da kuma tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.
A gefe guda, shugaban Kungiyar ci gaban Shanono/Bagwai, Alhaji Yahaya Bagobiri, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa ’yan bindigar sun zo ne da nufin ramuwar gayya bayan rasa mambobinsu a hannun sojoji a makon da ya gabata.
Ya ce: “’Yan bindigar sama da 50 ne a kan babura, kowanne babur na ɗauke da mutum uku dauke da manyan makamai, sun kai farmaki a Yankwada, Babanduhu da wasu ƙauyuka, suna harbi daga ƙarfe 1:00 na daren Alhamis har zuwa ƙarfe 5:00 na safiyar Juma’a, inda suka kashe mutum ɗaya.”
Sai dai ya yaba wa sojoji saboda hana ’yan bindigar shiga manyan garuruwa.
Bagobiri ya ce: “Sojoji sun fatattaki ’yan bindigar duk da cewa sun zo da manyan makamai, amma abin da suka yi nasara kawai shi ne satar shanu 100 da kashe mutum ɗaya.”
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da ƙarin makamai da kuma tura ƙarin jami’ai don ƙarfafa dakarun da ke bakin aiki.
(IN)
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link