Ma’aikatan jinya sun yi barazanar shiga yajin aiki a Kaduna
[ad_1]
Ma’aikatan jinya da unguwar zoma a Jihar Kaduna sun yi barazanar shiga yajin aiki saboda kin kara musu matsayi da hukumomin lafiya suka yi tsawon lokaci a jihar.
Barazanar ta fito ne daga jawabin sabuwar shekara da shugaban ƙungiyar (NANNM), reshen jihar, Kwamared Ishaku Yakubu ya gabatar, inda ya nuna takaici kan abin da ya kira kin kula da ci gaban ayyukan ma’aikatan jinya da unguwar zoma da Ma’aikatar Lafiya da wasu hukumominta suka yi.
Yakubu ya ce: “Mun fuskanci ƙalubale da dama, ciki har da kin gudanar da karin matsayi a Ma’aikatar Lafiya da wasu hukumominta,” yana mai cewa hakan ya shafi kwarin gwiwa da ingancin aiki a jihar.
Ya kara da cewa daga yanzu ƙungiyar ba za ta ƙara yarda da jinkiri da ke tauye ci gaban sana’a da mutuncinsu ba.
A cewarsa, ƙungiyar ta yanke shawarar ɗaukar mataki a sabuwar shekara. “A shekarar 2026, za mu ayyana dauki matakin shiga yajin aiki kan kin kara wa mambobinmu matsayi,” in ji shi.
Rigimar karin matsayin ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yajin aiki a cibiyar kula da kunne ta ƙasa da ke Kaduna, inda ma’aikatan jinya ke yajin aiki kan matsalolin da suka shafi matsayi da albashi.
Yakubu ya bayyana cewa yajin aikin, wanda ya shiga mako na biyu, ya samu cikakkiyar nasara. “Yajin aikin ya shiga mako na biyu kuma ya yi nasara 100 bisa 100,” in ji shi.
Ya gargadi cewa idan hukumomi ba su ɗauki mataki cikin gaggawa ba, hakan na iya jawo rufe cibiyoyin lafiyar gaba ɗaya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link