Ramadan: Za A Ci Gaba Da Bai Wa ‘Yan Wasa Musulmi Damar Buda Baki A Lokacin Buga Firimiyar Ingila

[ad_1]

A wannan shekarar ma, gasar firimiya ta Ingila da kuma English Football League za su ci gaba da aiwatar da tsarinsu na watan Ramadan, inda za a rika dakatar da wasa na dan lokaci, domin bai wa ‘yan wasa Musulmi damar buda baki. An fara Azumin watan Ramadan a wannan mako kuma zai dauki tsawon wata guda. A wannan lokaci, Musulmai na kaurace wa abinci da abin sha daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Da yake faduwar rana a Birtaniya tana tsakanin karfe 17:00 zuwa 19:00 agogon GMT a wannan lokaci, wasannin da za a iya dakatarwa zai fi shafar na ranar Asabar da karfe 17:30 da kuma na ranar Lahadi da karfe 16:30.

  • Ƴansanda Sun Gayyaci Bello Ado Bayero Kan Zargin Damfarar Kuɗin Fili Naira Miliyan 70
  • ’Yar Wasan Kasar Sin Gu Ailing Ta Kare Kambunta A Gasar Olympics Ta Milan Cortina

Kamar yadda aka saba a shekarun baya, shugabannin kungiyoyi tare da alkalai za su cimma matasaya kan lokacin da ya kamata a tsayar da wasan domin bai wa ‘yan wasa ko jami’ai Musulmi damar buda baki.

Kungiyoyi da alkalai za su tattauna tun kafin a fara wasa, domin cimma matsaya kan lokacin da ya kamata a dakatar da wasa domin bude bakin. Kuma ba za a tsayar da wasa ba a lokacin da ake gara kwallo, sai idan an samu damar bugun tazara ko jifa da dai sauransu. A shekarar 2021 ne aka cimma yarjejeniya da ta bai wa ‘yan wasa Musulmi damar buda baki yayin wasan Firimiya.

An kuma fara ne a wasa tsakanin Leicester City da Crystal Palace a watan Afrilu 2021. An dakatar da wasan a lokacin bugun falan daya a minti na 30 da fara wasan, domin bai wa Wesley Fofana na Leicester da Cheikhou Kouyate na Palace damar bude baki. Daga cikin sunayen ‘yan wasa Musulmi a gasar Firimiya akwai Mohamed Salah da William Saliba da Rayan Ait-Nouri da Amad Diallo da sauransu.

A shekarar 2023, tsohon dan wasan EBerton Abdoulaye Doucoure ya ce: A gasar Firimiya mutum yana da ‘yancin yin abin da ya dace. Ba za su taBa yin wani abu da ya saBa wa addininka ba, kuma wannan abu ne mai kyau. Ya ce yana azumi kullum, bai taBa kin yi ko da rana guda ba. Yanzu ya zama al’ada a gare shi, kuma abu ne mai sauki. Horarwa tana tafiya kamar yadda aka saba a Ramadan, amma idan sun je wasannin waje, suna iya cin abinci daga baya fiye da sauran ‘yan wasa, don haka mai girki yana shirya musu abinci yadda ya kamata, kamar yadda suke samu a gida. Suna samun abinci halal, don haka babu wata matsala.

Haka kuma a shekarar 2022, tsohon dan wasan LiBerpool Sadio Mane ya bayyana cewa kungiyarsa tana sauya jadawalin atisaye domin tallafa wa ‘yan wasa Musulmi a watan Ramadan wanda ya yabi shugabannin kungiyar da masu bayar da horo, sai dai kawo yanzu abun haka yake a kasashe da daman a duniya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *