Farfesa na Farko a fannin Ilimi a Arewa, Adamu Baikie, ya rasu yana da shekara 94

[ad_1]



Allah Ya yi wa Farfesa Adamu Baikie, wanda ya kasance Farfesa na farko a fannin Ilimi daga Arewacin Najeriya, rasuwa.

Farfesa Adamu Bakie ya rasu yana da shekaru 94 ne a daren Jumma’a a gidansa da ke Zariya, Jihar Kaduna.

Babban ɗansa, Manjo Muhammad Adamu (Ritaya), ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a sanar da jama’a cikakkun bayanai da lokacin da za a gudanar da jana’izarsa daga baya.

Baikie ya shahara sosai wajen gina fannin ilimi a Najeriya, inda ya yi aiki a manyan makarantu da dama.

Ya taɓa zama Shugaban Jami’a a wasu jami’o’in Najeriya, kuma ya jagoranci wata jami’a a Kudancin Afirka a lokacin aikinsa.

An haifi Farfesa Adamu Baikie ne a Wusasa, Zariya a 1931 saidai ya girma ne Sabon garin Kano, inda ya yi karatun firamare kafin daga baya ya dawo makarantar middle a Zaria a shekarar 1948.

Ya zama farfesa na farko a ɓangaren ilmi daga Arewacin Najeriya a 1971.

Ana kallon da a matsayin jigo wajen kafa tsare-tsaren koyar da malamai, tare da samar da gudummawar da ta ɗore a bangaren ilimi na Najeriya.

Ya rasu ya bar ’ya’ya biyar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *