Yarin Fika ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a Yobe
[ad_1]
Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar.
Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar.
Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar.
Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen goyon bayan jam’iyyar APC.
Ya ce, “Ina son ku gane cewa a halin yanzu, PDP da sauran jam’iyyun adawa a Yobe kamar sun ƙare.”
Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Yobe, Alhaji Mohammed Gadaka, ya bayyana zuwan Yarin Fika a matsayin babbar nasara ga jam’iyyar.
Ya ce, “Muna maraba da ku a cikin jam’iyyar, kuma za mu ba ku cikakkiyar damar da kowane mamba yake da ita. Za mu yi aiki tare da ku don ci gaban jam’iyyarmu.”
A nasa jawabin, Gwamna Buni ya nuna farin cikinsa da shigowar Yarin Fika da magoya bayansa.
Ya ce za su ci gaba da ƙoƙari wajen ci gaban jam’iyyar APC a Potiskum, da kuma dukkannin faɗin jihar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link