NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar ƙananan yara 10 a Taraba
[ad_1]
Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) reshen Jihar Taraba, ta kama wani da ake zargin safarar ƙananan yara 10 a garin Jalingo.
A cikin wata sanarwa da kwamandan hukumar na jihar, Malam Bako Amos, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an samu nasarar kama mutumin ne bayan samun bayanan sirri daga jama’a.
Ya bayyana cewa jami’an NAPTIP tare da haɗin gwiwar Mai Bai wa Gwamnan Jihar Taraba Shawara kan Safarar Mutane, Malama Sarah Ishaya, sun kama wanda ake zargin da misalin ƙarfe 11 na safe a Kurmi Park, Jalingo.
A cewarsa, mutumin yana shirin kai yaran zuwa wani waje da ba a sani ba.
Malam Bako Amos ya ƙara da cewa yanzu haka wanda ake zargin da yaran suna hannun NAPTIP, yayin da ake ci gaba da bincike.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link