Tarihin Rayuwar Hon. Aminu Suleiman A Takaice

[ad_1]

Masu iya magana sun ce, “In ka ji wane ba banza ba, in ba’a sha ruwa ba, an sha rana”

Hon. Aminu Suleiman shi ne Shugaban shahararriyar kungiyar magoya bayan Shugaba Tinubu mai suna “Tinubu Support Organisation (TSO)”. Shi ne ya kirkiro kungiyar kimanin shekaru Shida kafin Shugaba Tinubu ya furta maganar yin takarar Shugaban kasa domin nuna kauna ga shugaban da yada Manufofinsa na yin Takarar Shugabancin Nijeriya kasancewarsa mutumin da ya san halaye da dabi’un Shugaba Tinubu tun yana Gwamnan Jihar Legas.

  • CGI Babandede Mai Ritaya A Mizanin Kyawawan Halaye Da Kwazon Aiki
  • Gobara Ta Hallaka Mutum 2, Ta Lalata Dukiya Ta Biliyan 1.59 A Bauchi

Shi mutum ne zakakuri, jajirtacce, haziki mai kokari da himmar neman na kansa tun yana matashi. Yana da kokarin kamanta gaskiya da rikon amana. Yana da biyayya da da’a ga magabatansa da bin umarnin shugabanninsa a kodayaushe

Tarihin rayuwar Hon. Aminu Suleiman ya nuna cewa mutum ne wanda ya shafe kusan shekaru Talatin yana fafatawa da gwagwarmaya a aiyukan kwangila, safara, harkar mai da cinikaiya a sana’oi daban-daban a manyan biranen kasar nan tun daga lokacin mulkin soja har aka koma mulkin Dimokaradiyya. Bugu da kari, sabanin abun da wasu ke tunani, zuri’ar gidansu Hon. Aminu Suleiman na da rufin asiri, wanda sun mallaki kamfanin da ke hada-hadar mai, mai suna Bulasawa Petroleum wanda ya dade yana ta’ammalin cinikaiyar mai da Majalissar dokokin Nijeriya . Wannan na nuna cewa ba yau ya saba ganin kudi ko juya kudi ba.

Haka zalika, ya fara harkokin aiki a kamfanin Nasco a Legas tun 1991, lokacin mulkin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida. Sannan a lokacin mulkin Jenar Sani Abacha ma ya yi kwangiloli a kamfanin mai na NNPC, ya yi kwangilar gina Rijiyoyin birtsatse a rukunin gidajen NNPC da ke Abuja a lokacin da Marigayi Bar. Haruna Abubakar ke MD na PPMC

A lokacin da Hon. Aminu Suleiman ke zama a Legas, Wani mutumin Maiduguri mai suna Gwani Askira mazaunin Titin Abiola Crescent shi ne ya hada Hon. Aminu Suleiman da Marigayi Mashood Abiola ya gabatar da kansa gare cewa shi mutumin Kebbi ne kuma yana goyon bayan siyasarsa, daga nan suka saba, suka yi harkokin siyasa na wani lokaci har aka yi zabe ya fadi, sai ya dawo Abuja a shekara ta 1999 daga Abuja ya sake komawa Legas da Shugaba Tinubu ya zama Gwamnan Legas ya ci gaba da huddar arziki da shi ya zama dan cikin gida a gidan Shugaba Tinubu ya saba da iyalinsa da makarraban Gwamnatinsa, alaka tsakanin Shugaba Tinubu Gwamnan Legas a wancan lokacin da Hon. Aminu Suleiman ta zama tamkar ta Da da Uba,har daga bisani ya kirkiro kungiyar TSO ta girma, ta karbu a idon duniya, ta kuma ba da gudunmawa mai tasiri a zaben 2023 Shugaba Tinubu ya zama Shugaban kasa

Bayan kasancewar Tinubu zababbbe shugaban kasa, Hon. Aminu Suleiman bai sami kowanne irin mukami ba sai bayan shekara, Shugaba Tinubu ya bashi mukamin Shugaban Majalissar zartarwa na kwalejin fasahar kimiyya da ke jihar Nasarawa, sannan bayan watanni ya sake bashi mukamin Dan Majalissar zartarwa na sabuwar hukumar Raya shiyar Arewa maso yammacin Nijeriya. Idan aka duba za a ga cewa tagwayen mukaman da ya samu a sabbin ma’aikatu ne wanda ke bukatar lokaci da aiki kafin harkokinsu su daidata. Kwatsam sai ga wani abun mamaki mai kama da almara, wata kungiya da baaa san tushenta ba wai ” Concern TSO Pressure Proups” na kalubalantar Hon. Aminu Suleiman cewa ya yi watsi da Yayanta da samarwa kansa mukamai kuma kungiyar bata tabuka komai ga Yayanta ba.

Abun tambaya a nan shi ne suwa a ka yi watsi da su? Kuma ta yaya mutum zai bai wa kansa mukami kuma yaushe aka ba da mukamin kuma da aka ba da mukaman wanne aiki aka yi a ma’aikatun kuma me aka samu da har za a makance a yi suka ko korafi? Idan kuma akwai wanda yake da shedar cewa Honourable ya karbi wani kudi, to ya kawo sheda ko ya baiyana ta ga jama’a. Maganar gaskiya ita ce har yanzu a hukumar raya shiyar Arewa maso yammacin Nijeriya ba a saki kudi an yi wani takamaiman aikin da shugabanninta za su sami kudi ba. Kai ko harkokin daukar ma’aikata ba’a fara ba. Haka zalika a Kwalejin fasahar Keana nan ma ba magana, yanzu ake gina asalin filin makarantar na dindindin da maganar daukar daliban farko da fara sabon zangon karatu na farko a makarantar.

La’akari da haka,in dai ba hassada, kyashi da da bakinciki ake ba, za a gane cewa babu wani takamaiman aiki muhimmi da ma’aikatun ke yi wanda har wasu za su fara zargin ana samun wani abu ko an yi wani abu ba tare da su ba. Babu shakka, Duk wani yunkuri na suka ko korafi na nuna cewa lallai wannan mutane ba cikakkun ‘yan kungiyar TSO ba ne. Saboda tun daga zaben 2023 da Tinubu ya samu nasara kungiyar bata huta ba, tana ci gaba da ayyukanta yadda ta saba a cikin gida da wajen Nijeriya kuma tana samun nasarori.

A karshe akwai wasu zarge-zarge marasa tushe ballantana makama da bai kamata mu ce uffan akansu ba, saboda suna nuni da masu wadannan zarge-zarge ba asalin ‘yan kungiyar ba ne, in kuma har ‘yayanta ne, to sun yi nisa da ita kuma basa bibiyar harkokinta ka’in da na’in, sun koma gefe daya suna surutai marasa amfani da kokarin hana ruwa gudu da bata aikin da shugabanta da sauran Jajirtattun ‘yan kungiyar masu da’a da yi mata hidima ba dare ba rana ke yi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *