CMG Ya Kammala Bita Zagaye Na Uku Ta Shagalin Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Gargajiya Ta Kasar Sin
[ad_1]
A yau Asabar 31 ga watan Janairu ne, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya kammala bita zagaye na uku ta shagalin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, inda karon farko aka yi gwajin shirye-shirye a rassa hudu na shagalin, ciki har da birnin Harbin na lardin Heilongjiang, da birnin Yiwu na lardin Zhejiang, da birnin Hefei na lardin Anhui, gami da birnin Yibin na lardin Sichuan. Shirye-shirye da dama sun kara kayutatuwa sosai, ciki har da wake-wake, da raye-raye, da wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin, da wasan Kungfu da makamantansu, wadanda cikin annashuwa da farin ciki suka bayyana gagarumin ci gaban da kasar ta samu a sabon zamanin da muke ciki kuma a sabon tafarkin da kasar take bi. (Murtala Zhang)
[ad_2]
Source link