Han Zheng Ya Ziyarci Kasar Kenya
[ad_1]
Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya ziyarci Kenya bisa gayyatar takwaransa na kasar Kithure Kindiki, daga ranar 22 zuwa 25 ga watan Maris.
Yayin ziyarar, Han Zheng ya gana da shugaban Kenya William Ruto, kuma ya tattauna da mataimakin shugaban Kenya Kithure Kindiki. Sun yi musayar ra’ayoyi kan zurfafa dangantakar Sin da Kenya, da kuma bayar da fa’idodin bude kofa na shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15, sannan sun halarci bikin sanya hannu kan takardun hadin gwiwa.
Bugu da kari, Han Zheng ya gana da babban jami’in ofishin MDD a Nairobi da sauran shugabannin cibiyoyin MDD da ke Kenya a taron. Ya kuma halarci taron kasuwanci na Sin da Kenya tare da gabatar da jawabi, ya ziyarci bikin baje kolin kayayyakin Kenya da ke cin moriyar tsarin fitar da su zuwa Sin ba tare da biyan haraji ba, ya kuma duba cibiyar kula da zirga-zirgar jirgin kasa na Mombasa-Nairobi, sannan ya halarci bikin ban kwana da jirgin kasa na farko dake jigilar kayayyakin da Sin za ta shigo da su ba tare da biya masu haraji ba.(Amina Xu)
[ad_2]
Source link